Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya bukaci Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) tare da Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro (NSA) da su gudanar da bincike na musamman domin gano tare da hukunta masu yaɗa jita-jitar cewa ya rasu.
Sanata Akpabio ya bayyana cewa abin takaici ne kuma abin Allah-wadai yadda wasu ke yaɗa jita-jitar rasuwar mutane, musamman manyan ƴan siyasa, ƴan kasuwa da sauran fitattun mutane a cikin al’umma.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/huduba-babu-abin-da-ke-lalata-imani-kamar-shirkashi-ya-sa-hankalinmu-ke-tashi-kanta-dr-kabiru-gombe/
Ya ce irin wannan jita-jita ba wai kawai tana tayar da hankalin jama’a ba ne, har ma tana haddasa damuwa ga iyalai da masoya waɗanda abin ya shafa.
A kwanakin baya-bayannan ne wasu kafafen yaɗa labarai na yanar gizo suka wallafa rahotannin da ke cewa Sanata Akpabio na fama da matsananciyar rashin lafiya, inda har aka kwantar da shi a wani asibiti da ke birnin Landan, lamarin da ya ce ba gaskiya ba ne.

