Kungiyar anoman Najeriya ta bayyana damuwa kan yadda shinkafa da masara daga kasashen waje ke mamaye kasuwannin cikin gida, lamarin da suka ce na barazana ga cigaban noma a kasar nan.
Manoman sun bayyana hakan ne a sakonnin da suka wallafa a shafin sada zumunta na X, inda suka zargi manufar gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu da kawo cikas ga noman cikin gida.
Sun ce saukin harajin shigo da kayan abinci da gwamnatin tarayya ta bayar ya janyo faduwar farashin kayan abinci, amma hakan yana cutar da masu noma a gida.
TST Hausa ta rawaito cewa manoman sunyi gargadin cewa idan har noma ya durkushe a Arewa to Tinubu ne sila
A watan Yulin shekarar 2024 ne gwamnatin tarayya ta sanar da amincewar shigo da kayan abinci kamar shinkafa da masara ba tare da biyan haraji ba, na tsawon kwanaki 150.
Kwanturola-Janar na Kwastam, Bashir Adeniyi, ya bayyana cewa wannan manufa ta taimaka wajen rage farashin kayan abinci a kasuwanni.
Binciken da DAILY POST ta gudanar a kasuwanni ya nuna cewa buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 yana tsakanin ₦65,000 zuwa ₦68,000, yayin da masara ke sayarwa tsakanin ₦35,000 zuwa ₦37,000. Sai dai shinkafa daga waje na kai har ₦83,000 a buhu. Wannan saukin farashi ya janyo ragin ribar da manoma ke samu, tare da hana su kwarin gwiwar cigaba da noma.
Abin da ya kara tabarbarewar lamarin shi ne tashin gwauron zabon farashin taki, wanda ya janyo karin kudin samar da amfanin gona, kuma ya kara dagula halin da manoman ke ciki.
Da yake tsokaci kan lamarin, Farfesa Godwin Oyedokun daga Jami’ar Lead City da ke Ibadan ya bayyana cewa yawan kayan amfanin gona da ake shigo da su daga kasashen waje zai iya sa manoman Najeriya su daina sana’ar gaba daya. Ya ce kayan da ake shigo da su da arha daga waje na janyo gasa mai tsauri da manoma na cikin gida ba za su iya jurewa ba.
Masu ruwa da tsaki a harkar noma na kira ga gwamnatin tarayya da ta sake duba wannan manufa tare da samar da kariya ga manoman cikin gida domin kare harkar noma a kasar.

