Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (ICPC) reshen jihohin Kano da Jigawa ta sanar da fara shirin bibiyar ayyukan mazabu da ‘yan majalisar tarayya ke sanyawa cikin kasafin kuɗin ƙasa a duk shekara, domin tabbatar da cewa an aiwatar da su yadda aka tsara kuma al’umma sun amfana da su.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/babu-wanda-ya-kama-ni-ni-na-kai-kaina-efcc-inji-tsohon-jamiin-nnpc/
Shugaban ICPC na Kano da Jigawa, Barista Ahmad Muhammad Wada, wanda ya shaida hakan a ganawarsa da manema labarai ya ce daukar matakin na daga cikin kokarin hukumar na tabbatar da gaskiya, da rikon amana da kuma hana karkatar da kudaden jama’a da aka ware domin ayyukan raya mazabu.
Ya ce za su gudanar da ziyarce-ziyarce zuwa wuraren da aka ce an aiwatar da ayyukan,a Kano domin duba ayyuka 69 domin tantance ko an yi su bisa ka’ida, daidai da abin da ke cikin kasafin kuɗi, tare da duba inganci da amfanin da al’umma ke samu daga cikinsu.
Barista Wada ya jaddada cewa ICPC ba za ta lamunci duk wani yunkuri na karkatar da kudade ko aiwatar da ayyukan a takarda kawai ba tare da an yi su a zahiri ba.
Yace a Jigawa akwai ayyukan yan majalisar tarayya guda 36 da zasu duba ko anyi ko ba’ayi ba.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su bayar da hadin kai ta hanyar sanar da hukumar duk wani zargi ko koke da ya shafi ayyukan mazabu a yankunansu.
Barista Wada yace gaba daya kudaden da aka ware domin yiwa jama’a ayyukan raya kasa sun haura naira miliyan dubu 36.

