Hukumar kididdiga ta Najeriya NBS ta bayyana jihohin Enugu, da Kebbi, da Neja a matsayin jihohin da suka fi tsadar rayuwa a Najeriya.
Hukumar ta bayyana hakan a cikin kididdigar yanayin tsadar rayuwa da haihuwar farashin kayayyaki da ta fitar a watan Afrilu.
A cewar hukumar Jihar Enugu ce ke kan gaba wajen hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa a duk shekara, wanda ya kai kaso 35.98 cikin 100 , sai Kebbi da kaso 35.13 cikin 100, sai kuma Naija mai kashi 34.85.
Wannan ya nuna cewa jihohin ukun sun sami hauhawar farashin kayayyaki mafi girma a Najeriya.
A gefe guda kuma hukumar ta NBS ta fitar da jihohi uku da rayuwa tafi sauki a duk Najeriya da suka hada da , jihar Ondo, ta dauki kaso 13.42 cikin 100 da Cross River, da kashi 17.11 cikin 100; da Kwara, da kashi 17.28 cikin 100.
Wannan na zuwa ne bayanda farashin kayayyaki a Najeriya ya ragu zuwa kashi 23.7 cikin 100 a cikin watan Afrilu.
TST Hausa ta rawaito cewa a watan Mayun 2024, NBS ta bayyana jihohin Kogi, Bauchi da Oyo a matsayin jihohin da sukafi tsadar rayuwa

