Mukaddashin Shugaban hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Najeriya Sylvester Nwakuche, ya ce za sun shirya daukar sabbin ma’aikata 5,000 aiki nan ba da jimawa ba domin bunkasa ayyukansu.
Ya shaida hakan ne a lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar wakilai mai kula da hukumomin gyaran hali na Najeriya karkashin jagorancin dan majalisar wakilai Chinedu Ogar, domin kare kasafin kudin hukumarsa na shekarar 2025.
Nwakuche ya ce a watan Agustan 2024 shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya ba da izinin daukar ma’aikata 5,000 aiki a hukumar kula da gyaran hali.
Sai dai ya sanar da ‘yan majalisar cewa an dage daukar ma’aikata ne saboda rashin samun kudi.
Yan majalisar ta wakilai musamman wasu daga jihar Anambra dake cikin kwamatin kula da hukumar gyaran hali sun bayyana damuwarsu game da jinkirin da aka samu wajen daukar sabbin ma’aikatan.
Yan majalisar sun bukaci hukumar gyaran hali da ta hada kai da kwamitinsu domin ganin an gaggauta aiwatar da shirin daukar aikin akan lokaci

