Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano ta fara rabon jakunkunan hannu da kayan sawa ga maniyyatan bana a fadin jihar, a wani bangare na shirye-shiryen gudanar da aikin Hajji.
Darakta Janar na hukumar, Alhaji Abubakar Ibrahim Matawalle, ne ya kaddamar da rabon kayan, kamar yadda mai magana da yawun hukumar Suleiman A Dederi ya sanar inda ya bayyana cewa shirin na da nufin tabbatar da cewa dukkan maniyyata sun samu cikakken shiri kafin tafiyarsu zuwa kasa mai tsarki.
Ya ce hukumar ta dauki matakan da suka dace domin ganin an gudanar da rabon cikin tsari da kuma isar da kayayyakin ga maniyyata a dukkan kananan hukumomi cikin lokaci.
Hakazalika, ya yi kira ga jami’an cibiyoyin Hajji da su tabbatar da an gudanar da rabon cikin gaskiya da adalci, tare da tabbatar da cewa kowane maniyyaci ya karbi kayansa ba tare da wata matsala ba.
Alhaji Matawalle ya kuma bayyana cewa jihar Kano ta kammala dukkan matakan sarrafa da karbar bizar maniyyata, yana mai tabbatar da cewa an kammala shirye-shiryen da suka dace domin gudanar da aikin Hajjin bana cikin nasara.
Ya kara da cewa hukumar ta tanadi wadatattun kayayyaki da za su wadatar da dukkan maniyyatan da suka yi rajista, ba tare da an bar kowa a baya ba.
Kayayyakin da ake rabawa sun hada da jakunkunan hannu, kayan sawa na maza, zannuwa da hijabai ga mata, da kuma littattafan jagorar aikin Hajji domin taimakawa maniyyata yayin gudanar da ibadar.
Darakta Janar din ya kuma bukaci maniyyata da su kula da kayayyakin da aka basu tare da amfani da su yadda ya kamata domin saukaka musu gudanar da ibadarsu.

