Hukumar Jin daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta gano wasu maniyata guda biyu da ba za a ba su damar tafiya aikin Hajjin bana ba saboda rashin lafiya.
Babban Daraktan hukumar, Alhaji Abubakar Ibrahim Matawalle, ya bayyana haka ne a lokacin rufe Bitar Wayar da kan Maniyata da aka gudanar a makarantar SAS a Kano.
Duk da cewa Matawalle bai bayyana irin rashin lafiyar ba, amma yace cutar da aka gano suna dauke da ita ba zata basu damar yin Aikin hajji ba.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/gwamna-yusuf-ya-baiwa-mutumin-da-aka-kashewa-ya-ya-6-da-mata-kujerar-aikin-hajji-da-umara/
Yace an gano mutanan biyu ne wadanda daya ya kasance Namiji dayan kuma Mace a yayin tantance lafiyar Maniyatan da aka fara a makon jiya.
Ya kara da cewa hukumar na daukar matakan tabbatar da cewa duk maniyata da za su tafi Hajji sun kasance cikin koshin lafiya kafin tafiya.
Alhaji Matawalle ya kuma jaddada cewa adadin kujerun da aka bai wa jihar Kano a bana sunyi kadan, lamarin da ya sa ake bukatar hakuri da juriya daga maniyata yayin da ake tantancewa da shirya tafiyar Hajji.
KARIN LABARAIhttps://tsthausa.com/hajj-2026-hukumar-alhazai-ta-kano-ta-sanar-da-ranar-fara-allurar-rigakafi-da-binciken-lafiyar-maniyyata/
Yace a shekarar 1999 an baiwa Kano kujeru sama da dubu 10.
Hukumar ta ce duk maniyata za su ci gaba da samun cikakken horo da shiri kafin tafiya, domin tabbatar da aminci da nasarar aikin Hajji.
TST Hausa ta rawaito cewa Alhaji Abubakar Matawalle ya shaida cewa za’a cigaba da yiwa Alhazan na bana bita ta gidajen Radio da Talabijin duk da rufe taron bitar.

