Limamin masallacin Juma’a na Usman Bn Affan dake Unguwar Gadon Kaya Dr. Abdullah Usman Gadon Kaya, ya bayyana damuwa kan yadda matasan wannan zamani ke rufe Ido domin neman kuɗi ta kowacce hanya har suke saka kansu cikin caca,da harkokin crypto ba tare da cikakken ilimi ko fahimtar haɗarinsu ba.
Dr. Gadon Kaya yayi wannan jan hankali ne a yayin gabatar da hudubarsa ta ranar Juma’a.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/huduba-duk-gwamnatin-da-ba-ta-iya-kare-rayukan-jamaa-to-wannan-gwamnati-ba-ta-da-amfani-dr-aliyu-yunus/
Ya ce matsanancin son kuɗi ya sa matasa da manyan mutane mantawa da halal da haram, lamarin da ke haddasa asarar dukiya,da lalacewar tarbiyya da rikicewar zamantakewa.
Ya ce: “Caca da duk wata hanya ta samun riba cikin sauri ba tare da sanin halal ba, abin takaici ne kuma ya sabawa koyarwar addini.
Malamin yace hatta a kasuwanni yaran kasuwa suka zuba kudaden iyayen gidansu cikin Caca ba tare da sanin Iyayen gidan ba har takai ga kamfanonin da aka zuba kudin sun cuce su.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/huduba-rashin-kamun-kai-daga-mata-a-wannan-zamanin-alama-ce-ta-tashin-kiyama-dr-aliyu-yunus/
Dr. Gadon Kaya ya yi tsokaci kan harkokin crypto, inda ya bayyana cewa wasu matasa na kallonta a matsayin kasuwanci na zamani, amma rashin ilimi, rashin tsari da haɗarin da ke tattare da ita na jefa masu son kuɗi cikin matsala.
Yayi Allah wadarai da yadda Kamfanoni irin wadannan na Caca ke cutar da jama’a ciki harda kamfanonin sadarwa.
Ya kuma jaddada cewa arziki daga Allah yake, kuma samun kuɗi ta halal na buƙatar haƙuri,da aiki tuƙuru da dogaro da sana’o’i masu inganci.
Daga nan ya nemi matasa da kada masu irin wannan Caca su rudesu don sunga suna fantamawa da gina gidaje na alfarma.
Ya ce kuɗin da aka samu ta hanyoyin da ba su dace ba kan zama wata hanya ta kashe zukatan matasa su ta shi su nemi na kansu.
Malamin ya yi kira ga iyaye, da malamai da gwamnati da su ƙara wayar da kan matasa, tare da samar da horo, ilimi da damammakin sana’o’i, domin kare su daga hanyoyin da ka iya lalata rayuwarsu da makomarsu.

