Babban limamin Masallacin juma’a na Legas, Rudwan Jamiu, ya ce Shugaba Bola Tinubu bai baiwa ‘yan Najeriya kunya ba.
Malamin ya bayyana haka ne a lokacin da yake hudubar sallar Juma’a a babban masallacin Lekki da ke Legas, wanda shugaba Tinubu ya halarci sallar.
Limamin ya shaidawa Tinubu wanda yake sahun gaba cewa ,suna alfahari da Tinubun kuma sunayi masa fatan Alkairi a koda yaushe.
Limamin yace sune suka yiwa Shugaban kasa yakin neman zabensa a dan haka sun gansu da salon mulkinsa.
A hudubar tada,Malam Ruduwan yace suna godiya ga Allah ,tunda Tinubu bai yaudari yan Najeriya ba.
Daga nan ya roki yan Najeriya suci gaba da yiwa Shugaban kasa adua tare da bashi ikon sauke nauyin da yake kansa.
Sannan ya bukaci ‘yan Najeriya da su rika godiya ga Allah abisa ni’imar da Allah yayi musu na samun mutum kamar Tinubu.
Hudubar malamin da ta karkata kan yiwa Shugaban fatan Alkairi da yi masa adua,Malamin ya bukaci shugaban kasa da ya rika tunawa da soyayyar da yan Najeriya suke yi masa dan shima ya saka musu.
Your message has been sent

