Limamin masallacin Usman Bn Affan a unguwar Gadon Kaya cikin karamar hukumar Gwale a Kano Dr. Abdullah Usman Gadon Kaya, ya bayyana cewa yawaitar cin amana da yaudara a cikin al’umma na daga cikin manyan dalilan da suka hana ‘yan Najeriya jin daɗin rayuwa da samun ci gaba mai dorewa.
Malamin ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da hudubar sallar Juma’a, inda ya jaddada cewa wadannan halaye biyu sun zama ruwan dare a tsakanin jama’a, lamarin da ke haifar da matsaloli da dama a fannonin rayuwa.
Ya bada misali da yawan tauye Mudu da Algus da karya domin samun abin duniya.
A cewarsa, cin amana na nufin saba wa amanar da aka ɗora wa mutum, yayin da yaudara ke nufin ruɗin mutane domin samun wata riba ta haramtaciyar hanya.
Ya Kara dacewa da yawa daga cikin shugannni a Najeriya basa kishin wadanda suke mulka, illa ma dai a hada kai da su a cutar da mutane.
Malamin yayi gargadi kan yadda masu mulki suke neman mulki Ido Rufe, haka suma talakawa suke neman kudi ido rufe har ya kai ga wasu suna shiga caca.
A bangaren cin Amana “yace a yau zaka fito da mutum daga rana kasa shi cikin Inuwa amma wannan mutum shine na farko da zai fara cin amanarka”
Ya ƙara da cewa addinin Musulunci ya yi kakkausar suka ga waɗannan halaye, inda ya ambato hadisin Manzon Allah (SAW) cewa: “Wanda ya yaudare mu, ba ya cikinmu.”
Dr. Gadon Kaya ya ce illolin cin amana da yaudara sun haɗa da rugujewar tattalin arziki, rashin gaskiya a tsakanin jama’a, ƙaruwar talauci da kuma rashin tsaro. Ya ƙara da cewa waɗannan matsaloli na ci gaba da jefa al’umma cikin wahala tare da hana cigaban ƙasa.
Ya kuma yi kira ga kowane ɗan ƙasa da ya ɗauki alhakin gyara halayensa, ba tare da jingina komai ga shugabanni kaɗai ba.
A cewarsa, wajibi ne ma’aikata su riƙe amanar aikinsu, ‘yan kasuwa su guji yaudara, shugabanni su yi adalci, yayin da iyaye kuma su ba ‘ya’yansu tarbiyya mai kyau.
A ƙarshe, malamin ya jaddada cewa mafita ita ce komawa ga koyarwar addini, tsoron Allah da kuma tabbatar da gaskiya da riƙon amana a dukkan al’amura.
Ya nemi Al’umma da su gujewa aikata laifuka domin hakan na kwashe albarka da hana zubar ruwan sama da albarkatun kasa a cikin jama’a.
Ya kuma yi addu’ar Allah Ya gyara al’umma tare da sa a samu zaman lafiya da ci gaba a Najeriya.

