Limamin masallacin Juma’a na Jami’ar Northwest university dake Kano,Dr.Nasir Shu’aibu ya gargadi masu sakaci da Sallah ,wanda yace tun a duniya Allah yake tabar dasu kafin gobe Kiyama su hadu da fushinsa, mutukar basu tuba ba.
Dr Nasir wanda shine Na`ibin masallacin Juma’ar yayi wannan gargadin ne a hudubarsa ta Juma’ar nan ,mai taken “mahimmacin riko da Sallah akan lokacinta”
Dr. Nasir wanda malami ne a sashen koyar da addinin musulunci da harshen labarci na jami’ar Northwest a Kano, yace babu abu mai hadari a duniya tun kafin aje lahira, sama da wasa da sallah ko sakaci da ita ,ko kuma tozarta ta.
A hudubarsa tasa ,yace da yawa daga cikin mutane suna kallon kamar tilasta musu akayi su yi sallah, shiyasa wasu suke ganin kamar idan sunyi sallar sauke nauyi sukayi ba Ibada ba,koma sunyi ne domin samun lada ba.
Malamin yace a duniya babu wata ibada da Ubangiji ya dauka da mahimmaci wacce babu uzuri cikinta sama da sallah,Inda yace ,Allah bai daukewa Musulmi sallah ba mutukar akwai hankali a tare dashi,Amma yace sauran ibada,kamar azumi da zakka da zuwa aikin Hajji da sauransu , Ubangiji yana uzuri a cikinsu idan babu lafiya ko wata lalura daban.
Dr Nasir Shu’aibu a cikin hudubar tasa yace ,aikin mutum gaba daya yakan rushe,idan yana wasa da sallah ko tozarta ta , musamman sallar la’asar.
“MUNA GARGADI DA BABBAR MURYA GA MASU SAKACI DA SALLAH SUNA SANE , MUSAMMAN LA’ASAR WANDA MUTUM YAKAN RASA AYYUKANSA GABA DAYA NA ALHERI IDAN YA BARI TA WUCE SHI YANA SANE A RANAR”
Daga nan yace ko a kalamansa na karshe a rayuwarsa,Annabi Muhammad SAW yayi gargadi da hani da wasa da sallah da Kuma kiyaye ta akan lokacinta.
Malamin yaja hankalin iyaye da bayan sun kiyaye da sallah,to surika kuma kula da kiyaye sallar daga iyalansu ,domin tsira a duniya da gobe kiyama.
Dr Nasir ya kuma rantse da Ubangijinsa cewa ,duk masu kiyaye sallah da yinta yadda ya kamata,ba zasu taba yin talauci ba ko su tabe sannan akwai haske da zai rika wakana a fuskokinsu sannan, zasu tsira daga cutar zuciya da sauran gabobinsu.
Ya kuma gargadi masu tozarta sallah da su kiyaye haduwa da fushin Ubangiji sannan su tuba.
Yace masu tozarta sallah,sune wadanda basa yinta akan lokaci sai sunga dama ,da masu yinta yadda sukaga dama saboda suna da wani uzuri na duniya,da masu hada salloli biyu ko uku a lokaci daya,saboda uzurinsu na duniya.
Sannan yace ,yawanci irin wadannan mutane,suna tozarta sallah ne saboda shagala da kasuwanci ko neman abin duniya, alhalin kuma babu wani kasuwanci mai riba fiye da kulla kasuwanci tsakanin Allah da bawansa ,wanda kiyaye sallah na daga cikin kasuwanci mai riba tsakanin bawa da Ubangiji.
Dr Nasir yace ko damuwa mutum ya shiga , mutukar ya tsaida sallah,to Allah ya na bashi mafita.

