Limamin masallacin Juma’a na jami’ar Northwest dake birnin Kano Dr Nasir Shu’aibu yayi albishir na shiga Aljanna ga al’ummar musulmi musamman masu tsoron Allah da kuma siffantuwa da wasu halaye guda biyar.
Dr Nasir wanda malami ne a sashen nazarin ilimin harkokin addinin musulunci a jami’ar ta Northwest yayi wannan tsokaci ne a cikin hudubarsa ta ranar Juma’a 29 ga watan Sha’aban shekara ta 1446 bayan Hijra mai taken “maraba da Ramadan”.
Yace dukannin al’ummar musulmi suna son shiga Aljanna babu makawa,amma kuma akwai wani abu da Allah ya kebewa wasu bayinsa da yafi shiga Aljanna dadi shine ganin Allah a cikin Aljannar.
Malamin yaja hankalin alumma da su dage da ibada a cikin azumin Ramadan domin dacewa da duk wata falala da Allah yayiwa jama’a tanadi.
Dr Nasiru ya lissafo wasu halaye ko kuma ayyuka guda biyar da yace Allah ya na son masu aikata su ,tunda siffa ce ta Ubangiji ,kuma masu aikatawa sune Allah yake yayewa hijabi su ganshi shima ya gansu a gobe kiyama.
Dr Nasir Shu’aibu ya lissafo siffofin da yace sun hadu a cikin Aya guda a cikin Suratul Al-Imran Aya ta 134.
ٱلَّذِینَ یُنفِقُونَ فِی ٱلسَّرَّاۤءِ وَٱلضَّرَّاۤءِ وَٱلۡكَـٰظِمِینَ ٱلۡغَیۡظَ وَٱلۡعَافِینَ عَنِ ٱلنَّاسِۗ وَٱللَّهُ یُحِبُّ ٱلۡمُحۡسِنِینَ
1.Masu ciyar da dukiyarsu a cikin walwala ko kunci (Wato idan sun samu su ciyar idan sun samu hasara ko ba’a samu riba anan ma su ciyar da dukiyarsu ga mabukata musamman marayu da marasa hali.
2.Dr Nasir yace abu na biyu da Allah yake so kuma zaisa bayinsa su ganshi a Aljanna sune masu danne fushinsu idan sunyi fushi wanda yace wannan sufa ce ta Allah ita ma.
3.Sai na uku ,shine masu yin afuwa ga jama’a yan uwansu idan sun bata musu , alhalin suna da ikon ramawa.
4.Sai Kuma na hudu shine masu kyautatawa jama’a da yi musu hidima.
5.Cikon na biyar din kuma shine masu yawan tuba da yiwa Annabi Muhammad SAW salati.
Dr Nasir Shu’aibu yace masu siffantuwa da wadannan abubuwan sune Allah yake yaye hijabi tsakaninsa da su domin ganin Allah a cikin Aljanna wanda yafi shiga cikinta dadi.
Ya nemi jama’a da suyi amfani da wannan lokaci na azumin Ramadan domin dacewa da wannan dama.

