Mai Martaba Sarkin Kano,Malam Dr. Muhammadu Sanusi na II, ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su nemi yafiyar duk wanda suka ɓata wa a cikin watan Ramadan, yana mai jaddada cewa hakan na daga cikin ginshiƙan samun cikakkiyar lada da karɓuwar.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/huduba-rashin-kamun-kai-daga-mata-a-wannan-zamanin-alama-ce-ta-tashin-kiyama-dr-aliyu-yunus/
Sarkin ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da huduba a sabon Masallacin Juma’a da Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya samar a fadar gwamnatin jihar.
TST Hausa ta rawaito cewa manyan jami’an gwamnati,da malamai da yan siyasa da Shugaban ofishin karamin Jakadancin Saudiyya a Najeriya da sauran al’umma suka halarta.
A cikin hudubar tasa, Mai Martaba ya ce watan Ramadan wata ne na tsarkake zukata da gyaran halaye, yana mai cewa ibada ba za ta kammala ba matuƙar mutum na riƙe da fushi,da gaba ko sabani da wani.
“Duk wanda ya san ya ɓata wa wani, ko da da kalma ce ko da aiki, ya nemi yafiyarsa kafin wannan wata ya wuce,” in ji Sarkin.
Ya ƙara da cewa zaman lafiya da yafiya su ne ginshiƙan gina al’umma mai ƙarfi, tare da jan hankalin jama’a da su guji rikice-rikice da ɗaukar fansa, su rungumi sulhu da fahimtar juna.
KARINLABARAI:https://tsthausa.com/hudubamatasan-yanzu-idon-su-ya-rufe-da-neman-kudi-shiyasa-suke-saka-kansu-a-caca-da-crypto-dr-abdullah-gadon-kaya/
Haka kuma, ya tunatar da masu hali da su taimaka wa marasa galihu, musamman a wannan lokaci na azumi, domin rage musu radadin rayuwa da kuma ƙarfafa zumunci a tsakanin al’umma.
Daga nan,Sarkin ya yi addu’ar Allah Ya karɓi ibadar al’umma, Ya gafarta musu kura-kurensu, tare da ba su ikon ci gaba da kyawawan ayyuka bayan kammala watan Ramadan.
A karshe ya godewa Gwamna Abba Kabir Yusuf abisa samar da Masallacin da yayi yana mai cewa gina Masallacin da kula da shi abu ne mai mutukar mahimmaci.

