Hukumar Hisba ta jihar Kano ta kubutar da wata budurwa da ake zargin za a yi wa safarar zuwa ƙasar Saliyo.
TST Hausa ta rawaito cewa budurwar mai suna Sadiya Lawan yar asalin birnin Kano,mai shekara 18 anyi yunkurin tafiya da ita ne zuwa Kasar ta Saliyo bayan yada zango daga Kano zuwa Lagos zuwa kasar Benin daga nan zuwa Ghana sai kuma kasar ta Saliyo.
Tuni hukumar Hisba ta kama wacce ake zargi da safarar budurwar wato Fatima Muhammad domin tsaurara bincike.
Rahotanni sun nuna cewa hukumar ta samu bayanan sirri kan shirin tura budurwar zuwa ƙasashen waje ne ta hanyar wasu da suke dillacin matasa maza da mata da suka hada Khalifa dake Lagos da wani Aliyu.
Mataimakin babban kwamandan Hisba a Kano bangaren ayyuka na musamman Dr Mujahedeen Aminuddeñ Abubakar shine ya sanar da hakan a wani sakon murya da ya aikewa manema labarai ciki harda TST Hausa.
Hukumar Hisba ta kuma yi kira ga iyaye da al’umma su kasance masu lura da ‘ya’yansu tare da kai rahoto cikin gaggawa idan sun gano wata manufa da ta saba wa doka.

