Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya sake jaddada cewa tattalin arzikin kasar nan da tsaro sunfi ingantuwa a zamanin gwamnatinsa.
Buhari ya tabbatar da hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin Kungiyar wakilan kafafen yada labarai wato Corrospondent chapel na jihar Katsina a gidansa dake Daura.
Tsohon shugaban kasar ya jaddada cewa tsaro da tattalin arziki sun inganta sosai a Najeriya idan aka kwatanta da kafin zuwansa mulki a shekarar 2015 da Kuma bayan barinsa mulki a shekarar 2023 Inda komai ya koma baya.
Tsohon Shugaban na Najeriya yace abubuwa sun tabarbare bayan ya bar mulkin Najeriya.
Buhari ya kuma bayyana kwarin gwiwar cewa ci gaban da aka samu a lokacin shugabancinsa zai ci gaba da amfanar da Najeriya yana mai cewa, “Al’amura za su ci gaba da inganta anan gaba saboda abinda ya shuka na Alkairi.
Buhari ya kara dacewa har yanzu yan Najeriya na cigaba da cin gajiyar ayyukan raya kasa da ya samar a Kasar nan a zamanin mulkinsa.
Tsohon Shugaban yana wannan jawabi ne bayan da a baya bayan nan, shi kuma tsohon Sanatan Kaduna ta tsakkiya Shehu Sani a watan Yunin 2024 yace rashin tsaro ya fi muni a karkashin Shugaba Buhari fiye da gwamnatin Bola Ahmad Tinubu.
Hakazalika, a wata hira da aka yi da shi a gidan Talabijin na Channels a watan Satumbar 2024, shugaban jam’iyyar SDP na Najeriya Shehu Musa Gabam, ya yi ikirarin cewa tattalin arzikin Najeriya ya fi muni a zamanin Buhari fiye da gwamnatin Tinubu.
Jaridar DAILY POST ta bayar da rahoton cewa, a ‘yan watannin nan, hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya na ci gaba da hawa sama inda ya kaso 34.80 cikin dari a watan Disambar 2024, idan aka kwatanta da kaso 9.6 a karshen shekarar 2015.

