Kungiyar Kwadago ta Najeriya da kungiyoyin fararan hula sun yi kira da a kara rage farashin man fetur tare bukatarsu na ganin cewa ragin da aka samu na naira 935 duk lita a gidajen mai ya tabbata.
Idan ba’a manta ba matatar man Dangote tare da hadin gwiwar gidan mai na MRS ya sanar da fara sayar da man fetur akan naira 935 lita daga ranar litinin 23 ga watan Disamba 2024
Kafin sanarwar dai, an sayar da man fetur akan sama da Naira 1,030 a Legas da kewaye, yayin da aka sayar da shi fiye da Naira 1,060 a Abuja da jihohin Arewa.
Rahotanni nacewa cewa a ranar Lahadi, kungiyar dillalan man fetur ta Najeriya mai zaman kanta IPMAN ta ce za a fara siyar da man fetur a kan N935 a kowace lita daga ranar Litinin bisa la’akari da ragin da kamfanin Dangote ya billo dashi kuma shima kamfanin man fetur NNPCL ya aminta ya rage .
Saidai har yanzu yan Kungiyar Kwadago NLC na cigaba da zuba idanu dan ganin ragin ya fara aiki tun ranar litinin din saidai shuru babu wani gidan mai da yake sayarwa akan naira Marley 935 lita daya.
A wata takarda da wani babban jami’i a Kungiyar kwadago Mr Chris Onyeka ya fitar yace Kungiyar na Saka ido dan ganin ba a yaudari yan Najeriya akan ragin farashin man fetur din ba.

