Gwamnatin tarayya ta nemi yan Najeriya su yi azumin Kwana uku sannan su yi adu’oin neman daukin Allah domin magance matsalar karancin abinci a Najeriya da tsadar rayuwa.
Ma’aikatar noma da samar da abinci ta tarayyar Najeriya ce ta bayyana shirin fara azumin da addu’o’i na kwanaki uku domin neman daukin Allah madaukakin sarki a fannin noma da samar da abinci a kasar nan.
A cewar wata sanarwar sanarwa,mai dauke da sa hannun Darakta mai kula da albarkatun ma’aikatar, Misis Adedayo Modupe O.,tace ma’aikatar ta gayyaci dukinin masu ruwa da tsaki da sauran ma’aikata domin halartar taron adu’oin
Modupe ta ce taron addu’ar an shirya shi ne da nufin yin kira ga Allah da kuma goyon bayan kokarin gwamnati na tabbatar da tsarin samar da abinci mai dorewa a fadin kasar nan.
Sanarwar ba ta ambato ranakun fara azumin ba ,Amma ana ganin zai iya farawa daga litinin zuwa laraba.

