Gwamnatin tarayyar Najeriya ta gargadi yan kasuwa da su sauko da farashin kayan abincin da suke dashi domin hakan ya taimaka musu su sayar akan lokaci dan gudun hasara.
Gwamnatin tace kamar yadda farashin kayan abinci ya sauka kasa sosai a watan Janairu na shekarar 2025 da kaso 24 cikin 100 ya zama dole yan kasuwa su sauko da farashin kayan abincin.
Kamfanin dillancin labaru na kasa NAN ya rawaito cewa Ministan Noma da Albarkatun Kasa, Abubakar Kyari yayi gargadin a wajen bikin ranar nuna amfanin gona na alkama na shekarar 2025 da akayi a kauyen Dabi da ke karamar hukumar Ringim a jihar Jigawa.
Ministan wanda yayi Allah wadai da halin rashin kirki da wasu yan kasuwa ke nunawa a Najeriya na kin rage farashin kayan abincin idan an samu ragin Inda yace ,gwamnati ba zata lamunci hakan ba.
Yace a watannin bayan tsakanin watan Octoba zuwa Disambar shekarar 2024 an fuskanci tashin goron zabi na kayan abinci a Najeriya,Amma a yanzu bayan gwamnati ta dauki matakan fili dana boye ,kayan abincin ya sauka.
TST Hausa ta rawaito cewa a watannin baya ana sayar da buhun Fulawa Naira 81,000 amma yanzu tayi kasa zuwa N60,000, sai taliya ta kasar waje da Ministan yace a baya an sayar da ita sama da N20,000 yanzu ana sayar da ita N15,000.
Ministan yace ya kamata yan Najeriya su amfana da ragin da aka samu na kayan masarufi kamar yadda suke ji a jika idan an samu kari.

