Kwamishinan Kasa da tsare tsare na Kano Abduljabbar Muhammad Umar shine ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya kira a ofishinsa.
Kwamishinan ya ce wannan na daga cikin sabon tsarin da Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya billo dashi na kare kadarori musamman filaye a kano.
Yace tsarin ya zama wajibi idan akayi la’akari da yadda ake zargin mallakar filaye ba bisa ka’ida ba a kano
A ranar 25 ha watan Nuwanba ne Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da tsarin sabunta takardun filaye na C of O a ofishin maiakatar kasa ta Kano bayan bude wasu sabbin gine gine.
Rahotanni na cewa akwai filaye da dama da tsohowar gwamnatin Dr Abdullahi Umar Ganduje ta raba a kano tsakanin yan siyasa da sauran jami’an gwamnati da , kwamishinan yace dole a sabunta takardunsu da sauran filayen da aka mallaka

