Gwamnatin Jihar Kano ta yi bikin yaye wasu matasa da suka shiga aikin Daba su sama da 500 a Kano.
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Wayya shi ne ya jagoranci bikin a madadin gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf.
TST Hausa ta rawaito cewa an gudanar da bikin ne a dakin taro na ma’aikatar Sufuri ta jihar Kano.
Kwamishinan yace gwamna Yusuf ne ya sahale a rika gudanar da wannan shiri na tabbatar da cewa matasa sun rungumi zaman lafiya a jihar Kano wato safe corridor project.
Kwamishina Wayya wanda shine babban jami’in gudanarwa na kwamatin samar da zaman lafiya a jihar Kano,yace tsohon kwamishinan yan sanda na Kano CP Husaini Gumel ne ya samar da shi tun lokacin yana Kwamishina a Kano.
Daruruwan matasan da ake gani a yanzu,rukuni rukuni ne da shugabannin yan Daba da suka tuba,kuma kowanne a cikinku yana da mabiya ,wanda haka yace hakan ba karamar nasara ba ce , acewar Wayya.
A madadin gwamnan jihar Kano, Kwamared Wayya ya yabawa matasan saboda rungumar zaman Lafiya da su ka yi.
Yace kasancewar Kano ce ke Jagorantar jihohin Najeriya a kowanne bangare,bai kamata a rika rikice rikicen Daba da kwacen waya ba.
Ya tabbatarwa da mahalarta taron cewa su kansu matasan sun gaji da ayyukan Daba da kwacen waya a Kano.
Kwamishinan yaɗa labarai din yace gwamna Yusuf ya bada umarnin a fara tantance matasan da suka tuba domin basu dama a cikin ayyukan gwamnati sanann wasu a saka su cikin shirin samar da zaman lafiya da sauran tsare tsare da aka samar musu.
Haka zalika,Wayya yace akwai magungunan wanke zukata da hukumar NDLEA zata baiwa matasan da suka tuba dan warkewa daga abinda suka samu kansu a ciki a baya.
Sannan yace akwai wasu rukunin da za’a mayar makaranta domin samun ilimi mai inganci.
Daga nan kwamishinan ya roki yan Dabar da su rike tubansu da kyau tsakaninsu da Allah sannan su zamo mutanan kirki.
Mai Martaba sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi na II ya samu wakilcin sarkin shanun Kano,Alhaji Shehu Muhammad Dankadai.
Anasa jawabin kwamishinan yan sanda na Kano CP Ibrahim Adamu Bakori,ya nuna farin cikinsa da shirya taron,yana mai cewa abinda gwamnatin Kano ta kirkiro abin a yaba ne.
Yace bayan zuwansa Kano ya fahimci cewa ana shan kwayoyi da ayyukan Daba.
CP Bakori yace wannan ta sa ya samu gwamna Yusuf domin tabbatar da samar da shirin rungumar zaman lafiya a Kano.
Ya yabawa matasa abisa ajiye makamansu da su kayi.
Kwamatin samar da zaman lafiyar na Safe corridor project ya kunshi,wakilai daga kowanne bangare da suka had da shugabannin gargajiya da ma’aikata da jami’an tsaro da mataimakin Shugaban jami’ar Northwest Farfesa Muktar Atiku Kurawa da Kwamishinan yan sanda na Kano CP Ibrahim Adamu Bakori da Alhaji Gidado Muktar da sauransu.
