Gwamnatin Jihar Kano ta nuna alhini da mika ta’aziya ga gidan Radio Rahma da Talabijin a bisa rasuwar daya daga cikin ma’aikatansu Abubakar Dahiru Yakasai.
Kwamishinan yada labarai na Jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Wayya ya bayyyana hakan a madadin gwamnatin jihar Kano.
Yace ma’aikatar yada labarai da harkokin cikin gida ta jihar Kano tana mika sakon ta’aziyya ga mahukuntan gidan Radio Rahma saboda rasuwar Abubakar Dahiru Yakasai a ranar Alhamis.
Kwamishinan ya bayyana marigayi Abubakar Dahiru Yakasai a matsayin mai kwazo da nuna juriya da sha’awar aikin jarida wanda yace ya bar gibi a aikin Jarida musamman a inda yayi aiki kafin rasuwarsa.
A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na Jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Wayya ya sanyawa hannu da kansa ya bayyana mutuwar Dahiru Yakasai a matsayin babban rashi ba ga tashar Rahma Radio kadai ba harma tsakanin abokan aikinsa da masana’antar yada labarai.
Gwamnatin ta Kano ta jajantawa iyalan mamacin da yan uwa da abokan arziki tare da fatan Allah yaji kansa da gafara.
Abubakar Dahiru Yakasai ya rasu ne bayan gajeruwar rashin lafiya a Asibitin Nasarawa da ke birnin Kano.

