Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana damuwa kan ƙara yawaitar zurga-zurgar masu baburan haya (Achaba) a wasu sassan birnin Kano, duk da cewa har yanzu akwai haramcin da aka dade da kafa kan harkar.
A wata sanarwa da Kwamishinan yaɗa labarai da al’amuran cikin gida Kwamared Ibrahim Abdullahi Wayya ya fitar mai dauke da sa hannun daraktar hulɗa da jama’a da wayar da kai na ma’aikatar Sani Yola ya fitar ranar Lahadi, yace gwamnatin ta ce ta samu rahotanni masu karfi da suka tabbatar da dawowar Sana’ar Achaba a unguwanni daban-daban na Kano.
Haka kuma, wasu bayanan leƙen asiri sun nuna cewa wasu ƙananan hukumomi da kauyuka da ke kan iyakokin jihar sun fara fuskantar shigowar masu Achaba, ciki har da mutanen da ba a tantance asalinsu ba.
Sanarwar ta bayyana cewa akwai shigar wasu da ba a san su ba da ke amfani da babura suna bayyana kansu a matsayin masu haya, lamarin da gwamnati ta ce na iya zama barazana ga tsaro.
Gwamnatin Kano ta tabbatar da cewa tana daukar matakan da suka dace don kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tare da aiki tare da hukumomin tsaro a dukkan kananan hukumomi 44 na jihar.
“Mun samar da dukkan goyon bayan da ake bukata ga hukumomin tsaro don su gudanar da aikinsu cikin kwarewa, kuma gwamnati na shirye ta ƙara duk wani abu da ake bukata domin tabbatar da tsaro,” in ji sanarwar.
Ta ce duk shawarwarin jama’a, ciki har da ƙara sanya idanu a hanyoyin shiga da fice na jihar, na cikin abubuwan da ake nazarin aiwatarwa a sabon tsarin tsaro da ake duba.
Gwamnatin ta jinjinawa jama’ar Kano bisa hadin kai, kulawa, da irin rahotannin da suke bayarwa, tare da kira gare su da su kasance masu faɗakarwa da bayar da bayanai kan duk wani motsi da ake zargin na iya kawo barazana.
Sanarwar ta jaddada cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf zai ci gaba da aiki tare da kananan hukumomi, sarakunan gargajiya, shugabannin unguwanni da jami’an tsaro domin tabbatar da cikakken tsaro da zaman lafiya a fadin jihar.

