Gwamnatin Kano taci alwashin kawo karshen matsalolin da ake fama dasu a kogin wudil musamman sayar da gefen kogin ga wasu mutane ba bisa ka’ida ba.
Kwamishinan ma’aikatar ruwa ta jihar Kano Alhaji Umar Haruna Doguwa ya shaida hakan a wani taron masu ruwa da tsaki da ya kira,a game da matsalolin da ake samu a kogin Wudil.
Kwamishinan yayi gargadin cewa masu sayar da gefen gogin na Wudil,zasu fuskanci hukunci Kuma gwamnati na sane dasu.
Umar Haruna Doguwa ya bada misali da wani magidanci da aka sayarwa gefen kogin yake kiwon dabobi Kuma kashin shanu ke shiga cikin ruwan na Wudil.
Ya bayyana hakan a matsayin babbar barazana da ka iya haifar da cututtuka masu tarin yawa tsakanin al’ummar Kano da makota.
Yace ruwan na Wudil na daga cikin wanda ake tacewa a matatar ruwa ta Chalawa.
Ya kuma nemi masu hakar yashi da suma su koma karamar hukumar Wudil domin yi musu tsari mai kyau,ta yadda za’a rika kaucewa barazanar zaizayar kasa.
Anasa jawabin Shugaban karamar hukumar Wudil, Alhaji Abba Tukur ya nuna damuwarsa kan abinda ke faruwa a kogin na Wudil.
Ya tabbatarwa da kwamishinan ma’aikatar ruwa ta jihar Kano Alhaji Umar Haruna Doguwa cewa zasu hada hannu domin yaki da wannan matsala.
Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai Shugaban karamar hukumar Kumbotso Ghali Basaf da dan majalisar dokokin Kano mai wakiltar karamar hukumar Wudil Hon Musa Tahir.

