Gwamnatin jihar Kano ta jagoranci kaddamar da rabon Dabinon da kasar Saudiyya ta kawo Kano domin rabawa jama’a a lokacin watan azumin Ramadan.
Saudiyya ta aiko da Dabinon ne domin rabawa jama’a su yi amfani dashi lokacin buda baki.
A ayayinda yake jawabi wajen rabon Dabinon , Sakataren gwamnatin jihar Kano Alhaji Umar Faruq Ibrahim yace a duk shekara Saudiyya tana aiko da Dabinon ne domin rabawa jama’ar Kano a wani mataki na saukakawa jama’a.
Ya godewa gwamnatin ta kasar Saudiyya abisa wannan aiki da take na tallafawa jama’a.
Daga nan Sakataren gwamnatin Kano Alhaji Faruq yace a yanzu haka itama gwamnatin Kano ta ware naira miliyan dubu 8 domin ciyar da marasa karfi da masu bukata ta musamman abinci a lokacin buda baki.
A nasa jawabin jakadan Kasar Saudiyya a Najeriya Sheikh Khalil Ahamad Al-Adamawi yace kasar ta Saudiyya ta aiko da Dabinon katan 1,250 ga jama’ar Kano.
Ya nemi mutanan Kano da suyi amfani da Dabinon yadda ya kamata,kuma suyiwa kasar Saudiyya da Najeriya adu’a a lokacin azumin Ramadan dan samun zaman lafiya mai dorewa da karuwar arziki.

