Shugaban Hukumar shari’a ta jihar Kano Sheikh Abbas Abubakar Daneji,a madadin gwamnatin jihar,ya jagoranci kaddamar da kwamitocin da zasu tsara kalandar musulunci ta shekarar 1447 bayan Hijra domin amfanin jama’ar Kano.
An kaddamar da kwamitocin ne a harabar hukumar.
Sheikh Daneji yace wadannan kwamitoci ana umartarsu dasuyi aiki domin samar da kalandar kamar yadda aka saba a duk shekara.
Kwamitin farko wanda shine zai kula da samar da Kalandar zai kasance karkashin Shugabancin, Sheikh Abbas Abubakar Daneji.
Sai Kwamiti na biyu na samar da Ayoyi da Maudu’ai da za’a sanya karkashin Kwamishina na 1 Gwani Hadi.
Sai kuma Kwamitin samar da Hadisai da Hikimomi wanda zai kasance karkashin jagorancin kwamishina na 2 Sheikh Ali Danabba.
Da kuma Kwamitin dubawa da tabbatarwa karkashin Jagorancin Kwamishina na 1 Gwani Hadi.
Haka zalika akwai kuma Kwamitin Nisabi wanda Sheikh Ibrahim Falaqi zai shugabanta.
Sai Kwamitin raba kalanda karkashin Shugabancin, Umar Sani Mukhtar.
Baya ga Kwamitin Samar da Kalandar an kuma kaddamar da Kwamitin Bada Shawarwari na Ma’aurata da kuma Na tsaftar Muhalli.
A karshe Sheikh Abbas Daneji Ya kuma ja hankalin dukkanin Shugabbani da Mambobinsu dasu tsaya suyi aikin yadda ya kamata domin wannan aikin Al’umma ne bana Hukumar Shari’a ba.
Taron Kaddamarwar ya samu halartar kwamishinonin Hukumar da suka hada da Gwani Hadi da kuma Sheikh Ali Danabba da Daraktoci da Sauran Mambobin Hukumar.

