Gwamnatin Kano ta gurfanar da wani tela a gaban kotun Majestry karkashin jagorancin mai shari’a Halima A .B abisa samunsa da laifin hana makotansa sakewa.
Ma’aikatar kula da muhalli ta jihar ce ta kai ƙarar telan mai suna Mubarak Yusuf, kan yadda keken ɗinkinsa da kuma injin janaretonsa ke damun mutanen anguwa da daddare.
Wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar, ta ce duk da cewa ya musanta zargin, amma ta gabatar da hujjoji da suka gamsar da kotun.
TST Hausa ta rawaito cewa kotun bata tsaya nan ba saida ta kai ziyarar gani da ido shagon da telan ya ke dinki inda kuma ta tabbatar da cewa karar kekensa yana hana makotansa barci da daddare, abin da ya saɓa wa sashi na 7 na dokar kare lafiyar al’umma ta 2019.
“Don haka ne kotun ta yanke hukuncin taƙaita masa lokutan yin aiki, inda yanzu zai riƙa aiki daga karfe 6:00 na safe zuwa 9:00 na dare,” in ji sanarwar.
Duk dacewa Sanarwar bata ambata sunan unguwar da telan ya fito ba amma a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook ,Kwamishinan muhalli na jihar ta Kano, Dr Dahir Muhammad Hashim ya yaba wa kotun bisa wannan hukunci, inda ya ƙara nanata aniyar ma’aikatar na ganin ta tabbatar da kare muhalli a kano daga duk wata barazana, musamman gurbata muhalli da Iska ko ruwan shan jama’a.

