Gwamnatin Kano ta kuma yi Allah wadarai da kokarin da wasu keyi na haifar da rashin zaman lafiya a kano
Kwamishanan yada Labarai Hon Baba Halilu Dan Tiye MNI MON shine yayi wannan jawabin a wata sanarwa da ya fitar.
Yace gwamnatin Kano ta damu matuka da yadda aka rufewa sarkin Kano Muhammadu Sunusi na II kofar fita daga gidan sarauta na Rumfa.
Baba Halilu Dan Tiye yace wannan wani yun kuri ne na haifar da rikici a kano.
Ya nemi jami’ar Kano dasu kwantar da hankulansu .
Sannan gwamnatin Kano ta ce duk masu yiwa Kano mugun nufin da sannu a hankali zai koma kansu
A ranar Juma’a ne ,wasu jami’an tsaro na yan sanda da DSS suka yiwa gidan sarki na Rumfa kawanya tare da rufe kofar shiga gidan sarkin bayan da sarki Sunusi yayi yunkurin zuwa Bichi dan raka sabon hakimin karamar hukumar

