Gwamnan Jihar Abba Kabir Yusuf ya amince da rushe Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi tare da haɗa ta da Ma’aikatar Ilimi, a wani muhimmin mataki na ƙarfafa daidaito da kuma hanzarta sauye-sauye a fannin ilimi a Jihar Kano.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Darakta Janar na Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Gidan Gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Lahadi.
Mataiamakin gwamnan Jihar Kwamared Aminu Gwarzo shine yake jagorantar ma’aikatar a matsayin Kwamishina.
Sanarwar ta bayyana cewa bayan wannan sauyi, sabuwar ma’aikatar za ta ci gaba da aiki da sunan Ma’aikatar Ilimi, inda za a ƙirƙiri wani Sashen Kula da Ilimi Mai Zurfi wato (Directorate of Higher Education) a cikin ma’aikatar domin kula da harkokin jami’o’i da sauran cibiyoyin ilimi mai zurfi na jihar.
Za a naɗa Babban Sakatare (Permanent Secretary) domin jagorantar sashen, tare da samar da ma’aikatan da suka dace don tabbatar da ingantaccen gudanar da harkokin manyan makarantun gaba da sakandare.
Sanarwar ta ƙara da cewa, a ƙarƙashin sabon tsarin, dukkan hukumomin da ke ƙarƙashin tsohuwar Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi ciki har da Hukumar Tallafin Karatu ta Jihar Kano (Scholarship Board) — za su koma ƙarƙashin Ma’aikatar Ilimi. Haka kuma jami’o’in da gwamnatin jihar ke da su da sauran cibiyoyin ilimi mai zurfi za su kasance ƙarƙashin kulawar sabon sashen da aka kafa.
Gwamnatin jihar ta bayyana cewa wannan mataki wani ɓangare ne na shirin gyaran tsarin ilimi da take aiwatarwa domin sake farfaɗo da fannin, kawar da maimaita ayyuka tsakanin ma’aikatu, inganta daidaiton manufofi a dukkan matakan ilimi, da kuma rage kuɗin tafiyar da gwamnati.
Gwamna Yusuf ya jaddada cewa wannan sauyi an yi shi ne domin rage tsadar gudanar da gwamnati tare da ƙara inganci, gaskiya da kuma inganta tsarin tafiyar da harkokin ilimi a Jihar Kano.
Haka kuma, gwamnan ya sake tabbatar da kudirin gwamnatinsa na aiwatar da manyan sauye-sauye da za su farfaɗo da fannin ilimi tare da samar wa matasan jihar makoma mai kyau.
A ƙarshe, an umarci Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar da kuma Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnati su tabbatar da aiwatar da wannan sauyi cikin gaggawa da kuma yadda ya dace a dukkan ma’aikatun da abin ya shafa.

