Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya amince da tallafawa manoman da rikicin Boko Haram ya shafa ta hanyar rage musu farashin man fetur zuwa Naira 600 kowace lita.
A wata sanarwa da ta fito daga babban mataimaki na musamman kan sabbin kafafen yada labarai,ga gwamnan Borno wato Abdulrahman Bundi, ta ce Zulum ya sanar da tallafin ne a yayinda aka kaddamar da shirin raba kayan amfanin gona ga mamonan jihar.
Ya ce litar man fetur da ake sayarwa tsakanin naira 1,000 zuwa Naira 1,200 a Maiduguri yanzu za’a rika sayarwa manoma akan naira 600 duk lita domin taimaka musu a noman nasu musamman na rani.
Wannan dai na da nufin rage wa manoma matsalolin kudi da suke fuskanta a cikin al’ummomin da suka yi fama da barnar tattalin arziki da ababen more rayuwa a tsawon shekaru da aka kwashe ana rikicin Boko Haram.
Ya ce Zulum ya raba kayan amfanin gona da suka hada da buhu 2000 na hadadden takin NPK,da fanfuna 1000, da injunan bada ruwa guda 620.
A cewarsa, sauran kayayyakin sun hada da famfunan ruwa mai amfani da hasken rana guda 380, da na’urar feshin kwari guda 1000, da lita 1000 na maganin kashe kwari da iri, da dai sauransu.
Ya ce Zulum ya mika godiyarsa ga gwamnatin tarayya bisa gagarumin goyon bayan da gwamnatinsa ke bayarwa na sake ginawa da kuma tsugunar da al’ummomin da ta’addanci ya shafa.

