Gwamnatin Jihar Kano ta yaba da ƙoƙarin gidauniyar Islamic Charity Foundation da Better Life Women Education and Children Future Foundation bisa bayar da gudummawa ga mota kirar Toyota Coaster mai ɗaukar mutane 33 ga Ma’aikatar Jin Kai ta Jihar Kano, tare da ɗaukar nauyin horas da mata da matasa dubu goma (10,000) domin koyon sana’o’in dogaro da kai.
Gwamnan Jihar Kano,Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa tallafin ya dace da manufofin gwamnatinsa na inganta walwala da rayuwar al’umma, musamman yara almajirai, mata da matasa masu ƙaramin ƙarfi.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/gwamnatin-kano-ta-haramta-samar-da-hisba-mai-zamanta-kanta-a-jihar/
Shugabar Better Life Women Education and Children Future Foundation, Dr. Samira Abdullahi Abubakar, ce ta miƙa makullin motar ga gwamnan.
Ta ce an bayar da motar ne domin taimakawa ayyukan yau da kullum na kula da yara almajirai da gwamnatin Kano ta ciro daga titunan birnin Kano, domin ba su damar samun ilimin addini da na zamani tare da tarbiyya a ƙarƙashin kulawar Ma’aikatar Jin Kai ta Jihar Kano.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/kano-na-zaune-lafiya-ina-rokon-jamaa-su-daina-bari-ana-razana-su-gwamna-yusuf/
Ta ƙara da cewa shirin horas da mata da matasa dubu goma an ƙaddamar da shi ne domin rage talauci, ta hanyar koya wa al’umma sana’o’in dogaro da kai, lamarin da zai taimaka wajen inganta rayuwarsu.
Ta jaddada cewa wannan ba shi ne karo na farko da gidauniyar ke bayar da irin wannan tallafi ba, domin tallafawa masu ƙaramin ƙarfi na daga cikin manyan manufofinta.
Haka kuma, Dr. Samira ta bayyana cewa bayar da motar ya biyo bayan buƙatar da Kwamishinan Jin Kai na Jihar Kano, Alhaji Adamu Aliyu Kibiya, ya gabatar a lokacin wata ziyara da suka kai masa, inda ya nuna muhimmancin samun mota domin sauƙaƙa zirga-zirgar kai yara asibiti da gudanar da sauran muhimman ayyuka na yau da kullum.

