Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya amince da shigar da fursunonin Kano cikin shirin taimakekeniyar kula kiwon lafiya .
Wannan Shirin an tanadeshi ne kadai saboda ma’aikatan dake aiki karkashin gwamnatin Kano.
Saidai Gwamna Yusuf a yanzu ya amince da shigar da daurarrun gidan gyaran hali a kano ta yadda za a ba wa fursunonin damar samun ingantaccen shirin kula da lafiyarsu kyauta a lokacin da ake tsare dasu
Gwamnan na kano yace lafiyar fursunonin da kula da kiwon lafiyarsu na da mahimmaci a gwamnatinsa domin hakan zai tabbatar da samun kulawar da ake bukata a lokacin da ake tsare da su.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Kano CSC Musbahu Lawan Kofar Nasarawa ya rabawa manema labarai ciki harda TST Hausa yace gwamnan jihar Kano ya bayyana hakan ne ta bakin Shugabar hukumar kula da taimakekeniyar Lafiya ta Kano (KACHMA) Dokta Rahila Aliyu Muktar, a lokaciin da ta kai ziyara ofishin babban kwantirola ba hukumar gidajen gyaran hali ta Kano Ado Inuwa .
Ta kuma baiwa kwantirolan tabbacin cewa a shirye gwamnatin kano take wajen tallafawa da kuma taimaka wa dukkanin fursunonin da suke tsare a gidan hali a kano.
Ta nemi daurarrun da su rikawa gwamnatin kano adu’ar samun nasara .
Anasa jawabin Kwanturola Ado Inuwa, ya yabawa gwamnatin jihar bisa irin goyon baya da taimakon da take baiwa hukumar , ya kuma kara da bayyana cewa wannan karamcin zaisa daurarrun su rika kiyaye doka a da oda

