Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya raba babura ga wasu ’yan jarida da ke aiki a fadar gwamnatin Kano a wani mataki na tallafa musu da kuma nuna godiya ga rawar da suke takawa wajen yada labaran gwamnati.
Mai taimaka wa gwamnan na musamman kan kafafen sada zumunta, Salisu Muhammad Kosawa, ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook inda ya ce tallafin zai taimaka wajen saukaka musu zirga-zirga.
Wadanda suka ci gajiyar wannan tallafi sun hada da wakilan kafafen Rahma Radio, da Radio Kano da Radio Nigeria Pyramid da Nasara Radio da ARTV da kuma ma’aikata daga ma’aikatar yada labarai ta Kano .
Babban daraktan yada labarai na gwamnatin jihar, Kano Hon. Sanusi Bature Dawakin Tofa ne zai mika baburan a madadin gwamnan.
Daga cikin wadanda za su karbi baburan akwai:
Usman Gwadabe
Sani Surajo
Adamu Dabo
Tukur S. Tukur
Tijjani Sorondinki
Ibrahim Muazzam
Mubarak Ismail
Jabir Ali Dan Abba
Rabiu Sanusi
Muzammil Sanda
Khalid Yusuf
Jama’a a Kano sun yi maraba da wannan mataki tare da addu’ar cewa Allah ya saka wa gwamna da alheri, ya kuma dawo da shi akan mulki karo na gaba.
Ana sa ran na gaba za’a bada kashi na biyu har zuwa na uku ,domin kowa ya amfana.

