Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da naɗin wasu mutane a hukumomin gwamnatin Kano.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Kano Alhaji Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Juma’a yace dadin mutanan ya fara aiki nan take.
Daga cikin wadanda aka naɗa sun hada da:
1.Dr.Bashir A Muzakkar a matsayin babban daraktan hukumar kula da bunkasa harkokin sadarwa (KASITDA) kafin nadinsa shine mai baiwa gwamna Yusuf shawara kan fasahar tattalin arzikin na zamani.
2.Kabiru Sa’idu Dakata a matsayin shugaban hukumar tallace tallace ta Kano.
3.Dr Fatima Abdul Abubakar wacce gwamnan jihar Kano ya amince a matsayin shugabar hukumar kare hakkokin jama’a da zamantakewarsu.
4.Eng Isyaku Umar Kwa a matsayin mataimakin daraktan hukumar kula da gidaje ta jihar Kano.
5.Hamisu Musa Gambo Dan Zaki a matsayin shugaban hukumar bada tallafin Karatu ta jihar Kano.
6.Barista Isma’ila Nasarawa , Shugaban cibiyar koyar da yaki da cin hanci da rashawa.
7.Kaftain Muhammad Bello Maigaskiya Gabasawa mai ritaya,a matsayin kwamandan kwalejin horas da harkokin tsaro .
Sanarwar tace , gwamna Yusuf ya taya mutanan murna tare da nuna ganawarsa akan su.
Ya bukace su da suyi aiki tukuru domin sauke nauyin dake kansu.

