Gwamnatin jihar Kano ta karbi rahoton kwamatin binciken kwamishinan kula da harkokin sufuri na Jihar Kano Alhaji Ibrahim Namadi Dala.
A makon da ya gabata ne gwamna Yusuf ya kafa kwamatin domin binciken kwmashinan na sufuri da aka zarga da taka rawa wajen karbar belin dilan kwaya a Kano Danwawu Fagge daga babbar kotun jiha.
Sakataren gwamnatin Kano Alhaji Umar Farouk Ibrahim ne ya karbi rahoton a madadin gwamnatin Kano.
Sakataren gwamnatin Kano yace kamar yadda gwamna Yusuf yake takatsantsan wajen daukar mutum aiki a kowanne mataki a gwamnati haka yanzu ma ,idan an samu matsala da mutum sai anbi a hankali wajen daukar mataki domin yiwa kowanne bangare adalici,inda ya ce ba batu ne na gaggawa ba.
“Mun san cewa abin ya taba ran mutanan kano,kowa ya tofa albarkacin bakinsa ,mai kyau da akasin haka”,Inji Sakataren gwamnatin Kano
Ya tabbatar dacewa zai mika rahoton ga gwamna Abba Kabir Yusuf kuma nan gaba zai sanar da matsayin gwamnatin Kano akan lamarin.
A nasa jawabin shugaban kwamatin binciken da gwamna ya kafa, Barista Aminu Husaini yace sun tuntubi kowanne bangare kafin gabatar da rahoton.
Hukumomin da aka tuntuba acewarsa sun hada da DSS da NDLEA da Kungiyar lauyoyi ta kasa NBA da sauran masu ruwa da tsaki.
Haka kuma Barista Aminu yace ,sun gayyaci shi kansa kwamishinan na sufuri domin ji daga gareshi,kuma ya bada hadin kai.
Haka zalika, kwamatin yace ya karbi dukannin takardun shari’a daga babbar kotun jihar Kano,domin yin nazari akansu.
Yace sun mika rahoton domin gwamna Yusuf ya dauki mataki na gaba.
Yan kwamanti sun godewa gwamna Yusuf abisa yadda bai taka rawa ba ko yin katsalandan a aikin nasu.
A baya dai kwamishinan na Sufuri ya musanta dukannin zarge zargen da akeyi masa harma ya nemi afuwar jama’ar Kano.
A karshe Sakataren gwamnatin Kano Alhaji Umar Farouk ya rushe kwamatin saboda gama aiki da da yayi.

