Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya jagoranci raba tallafin Naira miliyan 400 ga kungiyoyin manoma goma dake jihar Kano a matsayin bashin da babu ruwa domin bunkasa samar da abinci a Kano.
Da yake raba takardun shaidar bada kuɗin ga kungiyoyin manoman a dakin taro na Coronation a gidan gwamnati, gwamna Abba Kabir Yusuf yace kuɗaden tallafi ne daga bankin duniya da hadin guiwar gwamnatin Kano a Karkashin kulawar hukumar yaki da sauyin yanayi da bunkasa noma da muhalli wato AcreAsal a jihar Kano.
Gwamnan yace manufar bada kuɗaden shine kyauta aikin noma da tabbatar da inganta muhalli da tattalin arzikin al’umma a wuraren da ake da matsalar karancin ruwa.
Daga nan ya nemi kungiyoyin da suyi kyakkyawan amfani da kudin ta fuskar zuba jari a harkokin noma da kiwo domin samar da abinci da habaka tattalin arzikin jihar Kano.
Gwamna Yusuf ya ce gwamnatinsa ta himmatu wajen yaki da kwararowar hamada da zaizayar kasa da dumamar yanayi da kuma gurbacewar muhalli.
Gwamnan ya Kara da cewa, gwamnatinsa ta samar da karin motocin kwashe shara domin tabbatar da tsaftar Mahalli a kasuwanni da cikin kwaryar birnin Kano.
Ya yi kira ga yan kasuwa dasu kaucewa dabi’ar zuba Shara a Kan tituna, inda yace gwamnati ba zata lamunci wannan mummunar dabi’a ba.
Sannan ya jinjinawa kwamishinan muhalli na jihar Kano Dr Dahir Muhammad Hashim abisa yadda ya samar da sauyi a Kano a bangaren inganta muhalli da tsafta.
Da yake jawabi tunda farko kwamishinan na muhalli da sauyin yanayi na Jihar Kano
Dr.Dahir M. Hashim ya ce ana fata kungiyoyin zasu dawo da kuɗaden akan lokacin da aka tsara tare da fatan nan gaba wadanda za’a baiwa sun ninka haka.
TST Hausa ta rawaito cewa kowacce kungiyar manoma daya ta samu Dala dubu 25 daga cikin kungiyoyi 10 da aka fara dasu.
Haka zalika gwamna Yusuf ya dakatar da duk wani rusau a garin na Rimin Zakara

