Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya dakatar da babban maitaimaka masa kan dauko rahotanni daga ma’aikatar sufuri ta Jihar Kano (SSR) Hon.Ibrahim Rabiu nan take saboda samunsa da laifin sakin bakinsa akan Madugun kwankwansiyya sanata Rabiu Musa kwankwaso ba tare da girmamawa ba.
Haka kuma gwamnatin Kano ta bukaci a baiwa wanda aka dakatar takardar tuhuma saboda zargin yin kalamai marasa dadi akan sauya Shekar Sanata Rabiu Musa kwankwaso wanda yayi su babu wata hujja.
Sakataren gwamnatin jiha Alhaji Umar Faruq Ibrahim shine ya aike da takardar dakatarwar wacce ke dauke da sa hannun daraktan yada labarai na gwamnan Kano Alhaji Sunusi Bature Dawakin Tofa.
Sanarwar ta kuma gargaɗi duk masu rike da mukaman siyasa da su rika kiyaye harshensu da gujewa furta kalaman da ba’a basu izini ba.
Sunusi Bature Dawakin Tofa ya shaida cewa gwamnatin Kano ta nesanta kanta da kalaman mai taimakawa gwamnan Kano da aka dakatar game da furucin da yayi na sauya Sheka da yace Sanata Rabiu Musa kwankwaso yayi,da kalaman da yayi marasa dadi.
Sanarwa tace Hon Ibrahim yayi kalaman ne abisa radin kansa kuma shi kadai yasan dalilansa nayin su .

