Gwamnatin jihar Kano ta sallami ma’aikatan wucin gadi na kasuwar Sabon Gari a birnin Kano albashin wata uku a jere da suke bin gwamnati.
Shugaban hukumar kasuwar Sabon Gari Alhaji Abdul Bashir Husaini ne ya bayyana hakan a yammacin ranar Alhamis.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar kasuwar ta Sabon Gari,Ado Haruna Muhammad ya rabawa manema labarai a birnin Kano yace an biya ma’aikatan wucin gadin ne saboda irin aikin da sukeyi dare da rana a kasuwar.
Alhaji Bashir Husaini yace tun bayan zuwansa a matsayin shugaban hukumar kasuwar Sabon Gari,ya gano cewa ma’aikatan wucin gadin suna bin gwamnatin da ta gabata ta Dr Abdullahi Umar Ganduje kuɗade masu tarin yawa.
Yace ba tare da bata lokaci ba ,hankalin gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kai kan wannan matsalar kuma ya fara aiki domin shawo kanta.
TST Hausa ta rawaito cewa gwamna Yusuf ya amince a baya ma’aikatan wucin gadin albashin watanni uku a jere ciki harda watan Yuni da ya kare.
“Watanni 18 ma’aikatan wucin gadin suke bin gwamnatin da ta gabata ta APC ,a karon farko aka biyasu watanni uku a jere , yanzu na kashi na biyu aka biya watanni uku ,har a kammala biyan bashin,”Inji sanarwar
Ma’aikatan dai sun cika da murna da Kuma godewa gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf.

