Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bada umarnin biyan albashin ma’aikata kafin Sallar karama.
Mai riƙon muƙamin Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Hajiya Bilkisu Shehu Maimota wacce ta sanar da hakan tace Gwamnan Jihar Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin a gaggauta sakin kuɗaɗen albashin ma’aikatan ne domin samun damar gudanar da bikin Eid al-Fitr cikin kwanciyar hankali.
Ta ce gwamnan ya ba da wannan umarni ne domin bai wa ma’aikatan gwamnati damar yin shirye-shiryen bikin Sallah cikin walwala tare da iyalansu.
Hajiya Maimota ta ƙara da cewa biyan albashin da wuri yana nuna yadda gwamnatin jihar ke kula da jin daɗin ma’aikata, tare da yabawa irin gudummawar da suke bayarwa wajen tafiyar da harkokin gwamnati da kuma ci gaban jihar Kano.
Har ila yau, ta yi kira ga ma’aikatan gwamnati da su yi amfani da wannan dama yadda ya dace, tare da ci gaba da nuna ƙwazo, gaskiya da kuma ladabi wajen gudanar da ayyukansu domin ci gaban jihar.
TST Hausa ta rawaito cewa ana sa ran yin bikin Sallah karama a ranar Alhamis ko Juma’a a makon da ake ciki

