Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf shida tawagarsa ,sun tashi zuwa birnin Madina dake Kasar Saudiyya domin jana’izar Dattijon attajiri Alhaji Aminu Alassan Dantata wanda ya rasu a daren Juma’a a Dubai.
Gwamna Yusuf shida tawagar ta sa sun tashi ne da Asubahin ranar Litinin 30 ga watan Yuni 2025.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Kano Alhaji Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar yace tawagar ta gwamna Yusuf ta hada da mai martaba sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi na II da gwamnan jigawa Alhaji Umar Namadi da tsohon gwamnan jihar ta Jigawa Alhaji Sa’ad Birnin Kudu da sauran manyan jami’an gwamnati.
Jim kadan kafin gwamna Yusuf ya bar birnin Kano zuwa Madina ,ya bayyyana marigayi Alhaji Aminu Dantata a matsayin uba ga kowa a Najeriya.
Yace zuwansa Madina shida tawagarsa ya nuna irin girmamawa da mutanan Kano da gwamnatin Kano suke yiwa marigayin musamman kasancewarsa Dattijo a Jihar.
TST Hausa ta rawaito cewa bayan wakilan gwamnatin Kano, wakilai daga gwamnatin tarayya da jiga jigan yan siyasa da manyan yan kasuwa zasu halarci jana’izar ta marigayi Alhaji Aminu Dantata a Madina.
A litinin din nan za’a binne gawarsa a Madina.
Tun kafin rasuwarsa ya baiwa iyalansa wasiyar cewa idan ya rasu a binne gawarsa a Madina kusa da uwar gidansa Hajiya Rabiatu Tajo Dantata.

