Galadiman Gezawa kuma kwamishina a hukumar zabe ta jihar Kano (KANSIEC) Alh Lawan Badamasi Gezawaya ya taya gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf murnar cika shekaru 62 a duniya, inda ya bayyana shi a matsayin shugaba mai hangen nesa wanda ya kawo sauyi mai inganci a jihar Kano.
A cikin wata sanarwa, Alh Lawan Badamasi, kwamishinan Yada Labarai da sauran al’amura na Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kano, ya yaba da irin nasarorin da Gwamna Yusuf ya samu a fannonin ilimi da lafiya da tattalin arziki da samar da ababen more rayuwa, inda ya ce hakan na nuni da irin kishi da jajircewarsa na ci gaban jihar Kano.
Ya yaba wa kokarin gwamnan, inda ya ce kwazon nasa ya zama abin koyi ga sauran gwamnoni kuma ya bar tarihi mai abin kwatance ga kowa.
A cewarsa, salon jagorancin Gwamna Yusuf ya sa jama’a ke girmama shi da kuma yaba masa.
Yunkurinsa na tabbatar da gaskiya da rikon amana da shugabanci na gari ya kawo sauyi mai kyau a jihar Kano.
Galadiman ya yaba da kokarin gwamnan na inganta harkar lafiya da inganta asibitoci, samar tsaftataccen ruwa da kayan aikin likitanci na zamani, da horar da ma’aikatan lafiya.
“Kokarin da ka yi a fannin ilimi, da suka hada da gina sabbin makarantu, gyaran da ake ma wa su, da samar da kayayyakin ilimi, ba za a bar su a bar su ba”. Inji Galadiman Gezawa.
Ya kuma yabawa gwamnan bisa irin tausayin da sadaukar dayake yi ga al’ummar jihar Kano, wadanda hakan ke tasiri a rayuwarsu ta hanyar jagoranci.
Daga nan ya taya al’ummar karamar hukumar Gezawa murna abisa ayyukan raya kasa da gwamna Yusuf ya samar a yankin.

