Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, zai yi hutu na tsawon mako uku domin kula da lafiyarsa.
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Bala Salisu Zango, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, inda ya ce gwamna Radda ya fada musu cewa, bai wa lafiyarsa muhimmanci abu ne mai matuƙar amfani domin ya ci gaba da gudanar da aiki yadda ya kamata da kuma yanke shawarar da ta dace ga jihar.
Sanarwar ta bayyana cewa Mataimakin Gwamna, Malam Faruk Lawal, zai rike ragamar mulkin jihar har zuwa dawowar gwamna Radda.
Gwamnan ya bayyana gamsuwarsa da ƙwarewar mataimakinsa wajen tafiyar da harkokin jihar, tare da tabbatar da cewa dukkan shirye-shirye da ayyukan ci gaba na jihar za su ci gaba ba tare da tangarda ba.
Sanarwar ta ƙara da cewa, gwamnati na sa ran dawowarsa cikin koshin lafiya domin ci gaba da yi wa al’ummar Katsina hidima.
TST Hausa ta rawaito cewa wasu daga cikin al’ummar jihar katsina na shakkun cewa ko gwamnan bai warke daga hadarin motar da yayi ba a ranar 20 ga watan Yulin shekarar 2025 akan hanyarsa ta zuwa Daura daga Katsina domin halartar adu’ar 7 ta marigayi Muhammadu Buhari.
Amma dai rahotanni sun nuna cewa gwamnatin ta Katsina bata bayyana rashin lafiyar ta gwamna Radda ba

