Gidauniyar Ambasada Sadiq A. Sule Garo ta tallafawa marayu da marasa karfi daga cikin magoya bayan jam’iyar NNPP da kayan sallah da Kuma kuɗin cefane.
TST Hausa ta rawaito cewa a kalla marayu da ya’yan jam’iyar NNPP guda 60 ne suka amfana da tallafin kayan sallah kyauta a garin Garo dake karamar hukumar Kabo a karshen mako.
Haka kuma an baiwa wasu kuɗi naira dubu biyar biyar kowannensu.
A yayinda yake karin haske ga manema labarai,shugaban gidauniyar ta Sule Garo wato Ambasada Sadiq Sule A.Garo yace ya bada tallafin ne a wani mataki na jin kai da kuma kyautatawa marasa karfi.
Ya kara dacewa bada tallafin,koyi ne ga madugun kwankwansiyya Sanata Rabiu Musa kwankwaso da gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf kan yadda suke jin kan al’umma.
Sadiq A Sule Garo wanda mataimaki na musamman ne ga Shugaban hukumar tsara taswirar Kano wato KANGIS Dr Dalhatu Sani Aliyu,yace a duk shekara yake bada tallafin ga marayu domin jansu a jika.

