Daga Ibrahim Aminu Makama
Gidauniyar Dahir Foundation ta gabatar da raba tallafin kayan karatu ga dalibai 200 a makarantar Sheikh Dahiru Usman Bauchi dake Gora Dansaka, karamar hukumar Malumfashi, Jihar Katsina.
Wannan tallafi ya gudana ne Rana ta yau 5 ga watan Janairu, 2025,
Shirin na daga cikin yunkurin gidauniyar wajen inganta ilimi da tallafawa matasa domin ciyar da al’umma gaba.
Wannan gidauniya ta rarraba kayan karatun da suka hada da litattafai, kayan rubutu, da sauran abubuwan da dalibai ke bukata don saukaka musu harkokin karatu.
Tallafin Bai tsaya ba a iya dalibai har ita kanta makaranta ta Samu tallafi kayan aiki Wanda zai amfanar da ita kanta makaranta na yau da kullum,
Tsarin ayyukan gidauniyar Dahir foundation tayi alkawarin zagaye jahohin na Nigeria domin Bada tallafi ilimi na Yara masu tasowa domin Gina future dinsu.

