Rahotanni na nuni da cewa a yan kwanakin nan wasu saƙonni da hotuna sun yadu a kafafen sada zumunta dake ikirarin cewa tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami, yana shirin auren Hajiya Aisha Buhari, matar marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.
Binciken gaskiya da gidan Jaridar PR Nigeria ya gudanar ya nuna cewa wannan zargi ba shi da tushe balle makama.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/buduba-cin-amana-da-yaudara-na-daga-cikin-abinda-zai-sa-allah-ya-zare-hannunsa-akan-mutum-ko-waye-farfesa-pantami/
Binciken ya gano cewa babu wata sanarwa ta hukuma, ko daga Pantami ko daga Aisha Buhari, da ke nuna cewa akwai batun aure a tsakaninsu.
Haka kuma, babu wani sahihin labari daga na kusa da su da ya nuna wani bayani da ke tabbatar da wannan ikirari.
Har ila yau, hoton da ake yadawa a matsayin hoton kafin aure wato “pre-wedding” ya nuna alamun cewa an kirkire shi ne ta hanyar fasahar (AI), wato ba hoto ne na gaskiya ba.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/na-yafewa-marigayi-buhari-duk-sabanin-da-ya-shiga-tsakaninmu-da-laifin-da-yayi-min-buba-galadima/
Wasu mutane da ke kusa da iyalan Buhari sun fito fili sun musanta labarin, suna bayyana shi a matsayin ƙarya da jita-jita da aka kirkira domin yaudarar jama’a.
Bisa dukkan hujjojin da aka tattara, an tabbatar da cewa labarin auren Isa Ali Pantami da Aisha Buhari ƙarya ne kuma mai ruɗarwa.
Jama’a na da bukatar su rika tantance sahihancin labari kafin yadawa, musamman a kafafen sada zumunta.
TST Hausa ta rawaito cewa a kwanakin baya an danganta Aisha Buhari da wani labari wanda shima bashida tushe inda akace Aisha Buhari na ikirarin fallasa wani babban malamin Addini a Arewa dake neman aurenta, idan har bai janye ba.
Amma a baya Aisha Buhari ta shaida cewa bata da niyar yin wani Auren anan gaba bayan rasuwar Muhammadu Buhari

