Jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta bayyana shirinta na tarbar Gwamna Abba Kabir Yusuf idan ya yanke shawarar barin NNPP ya koma APC, abin da ke tayar da cece-kuce a siyasar jihar.
Rahotanni na cewa gwamnan na shirin canza sheƙa zuwa APC nan da farkon watan Janairu 2026, musamman domin shirye-shiryen babban zabe na 2027.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/nnpp-ta-kori-shugaban-jamiyyar-na-kano-hashimu-dungurawanan-take/
TST Hausa ta rawaito cewa wannan batu ya jawo muhawara tsakanin shugabannin siyasa da magoya baya a jihar.
A cikin wata sanarwa da shugaban APC na Kano Abdullahi Abbas ya fitar yace Shugabannin APC a Kano sun bayyana cewa shiga gwamnan jam’iyyar zai ƙara ƙarfin APC a jihar, musamman wajen samun rinjaye a zaben 2027, inda suke ganin wannan mataki zai bai wa jam’iyyar fa’ida sosai.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/an-nada-hon-abdullahi-abiya-a-matsayin-shugaban-riko-na-jamiyyar-nnpp-a-kano/
Sai dai jam’iyyar NNPP a jihar ta bayyana cewa ba za ta amince da wannan shiri ba. NNPP ta yi kira ga gwamnan da ya ci gaba da kasancewa a jam’iyyar, tana mai cewa barin jam’iyyar zai zama cin amanar ƙuri’un masu zabe.
Masana siyasa na cewa wannan motsi na iya sauya taswirar siyasa a Kano, inda APC ke shirin amfani da damar wajen ƙara tasiri a tsakanin al’umma kafin babban zabe na shekara mai zuwa.

