Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Sa’ad III ya tabbatar da ganin jinjirin watan Shawwal a Najeriya a yau Asabar
Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III ya ce ganin jinjirin watan da aka yi ya sanya ranar Lahadi 30 ga watan Maris,na shekarar 2025 ta zamo 1 ga watan Shawwal, 1446.
Kwamitin tantance ganin wata karkashin jagorancin Mai girma Wazirin Sakkwato Farfesa Sambo Wali Junaidu ne ya jagoranci aikin tabbatar da ganin watan a bana.
Cikin sanarwar da ya yi Sarkin Musulmi ya ce “mun samu bayanai daga wurare daban-daban a Najeriya kuma mun zauna da masana domin tabbatar da ingancin waɗannan bayanan gabanin mu sanar da al’umma cewa an ga watan.
Ya nemi al’ummar musulmi da su yi amfani da bukukuwan Sallah wajen yiwa Najeriya adu’ar zaman lafiya mai dorewa.

