Jam’iyyar adawa ta PDP tace duk wani dan Arewa da yasan ciwon kansa ba zai yiwa jam’iyyar APC yakin neman zabe ko goyon bayan ta ba a zaɓen shekarar 2027.
PDP ta bayyana hakan ne a matsayin martani kan zargin cewa Sanata Lawal Adamu, dan majalisar dattawa mai wakiltar Kaduna ta tsakiya,daga jam’iyar PDP baya aikin komai sai ɗumama kujera.
Kalaman da alama ya fusata PDP,Inda jam’iyyar tace duk lalacewar PDP tafi APC aiki da saukakawa yan Najeriya.
Haka kuma, ana zargin gwamnatin Jihar Kaduna da dakatar da rarraba kayayyakin koyarwa da Sanata Lawal Adamu ya saya domin amfanin makarantun jihar.
Mataimaki na Musamman ga Shugaban PDP na kasa kan Yaɗa Labarai Yusuf Dingyadi ya ce ya kamata gwamnatin jihar ta haɗa kai da wakilan jama’a domin cigaban al’umma maimakon hamayya ta siyasa.
Jaridar Daily Truth ta rawaito cewa Dingyadi ya shawarci gwamna Uba Sani da kada ya bari wasu ’yan siyasa su ruɗe shi.
Ya ƙara da cewa,yan majalisar da PDP ta zaɓa suna aiki tuƙuru a jihar.
Yace suna yin ƙoƙari a yankunansu sama da na APC.

