Shugaban majalisar Malamai ta Arewacin Najeriya, Sheikh Malam Ibrahim Khalil yayi gargadin cewa dole ne duk wanda yaje sallar Idi yaki zuwa sallar Juma’a to ya sa ni cewa ya sabawa Allah.
Malamin ya bayyana hakan ne a shiri na musamman da aka gabatar dashi a gidan Radiyo Rahma Kano.
Malamin ya nuna mamakinsa kan yadda Malamai ke rudar da jama’a akan abinda ya ke ba wajibi ba ,abinda yake wajibi kuma a rika dauke hankalinsu akai.
“Hadisin dake cewa ba dole ba ne wanda ya yi sallar Idi ba sai yayi sallar Juma’a ,idan Idi ya zo a ranar Juma’a,Hadisi ne da aka shafeshi a yanzu,tunda yayi aiki ne lokacin rayuwar Annabi Muhammad SAW,tun yana raye da ya nemi mutanan dake wajen Madina (Kauye)da su zauna a gida ba sai sun dawo sallar Juma’a ba ,tunda su na da nisa, lokacin da sallar Idi ta hadu da Juma’a,”Inji Malam Ibrahim Khalil.
Ya kara dacewa a irin wannan zamanin masallatan Juma’a sun yawaita a ko ina a dan haka Wannan hadisin ba zaiyi aiki akan mutanan yanzu ba.
Ya nemi duk wanda yaje sallar Idi gobe Juma’a to wajibi ne yaje sallar Juma’a,idan kuwa yaki to ya sabawa Allah.
Ya nemi Malaman addini su daina rudar da jama’a akan abubuwan da zasu iya halakar da mutane idan basu aikata su ba.

