Mai Martaba Sarkin Kano,Malam Muhammadu Sanusi II, ya bayyana damuwarsa matuka kan yadda ake kara samun karuwar cin zarafin mata da fyade a jihar Kano, inda ya bukaci hukunci mai tsauri kan masu aikata wannan mummunar dabi’a tare da jaddada cewa addinin Musulunci ba ya amincewa da dukan mace.
Sarkin ya bayyana haka ne a fadarsa a ranar Litinin, 21 ga Yuli, yayin da ya karɓi bakuncin wakilan cibiyar bunkasa bincike kan cigaban mata da cibiyar wayar da kai da shiga tsakani a mahangar addinin musulunci na Jami’ar Bayero, Kano.
“Ni ban taɓa yarda da dukan mace ba, kuma masu dukanta ba su yin hakan don gyara halayenta,” in ji Sarkin. “Abin da muke gani a yau shi ne duka mai tsanani da raunata mata a sunan gyara.”
Ya ci gaba da cewa: “Addinin Musulunci shi ne ya fi kowa girmama mace. Wanda ke dukar matarsa har ya ji mata rauni ba mutumin kirki ba ne. Ba ni na faɗa ba—Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ne ya faɗa. Wadanda ba sa karatu su ne ba su san haka ba.”
Sanusi ya jaddada cewa malamai da limamai na da rawar gani sosai wajen dakile wannan matsala a cikin al’umma, inda ya bukaci su rika amfani da mimbarori wajen ilmantar da mutane game da darajar mata a cikin Musulunci.
Ziyarar da DRPC da CICID suka kai fadarsa na cikin wani shiri da Ford Foundation ke daukar nauyi, wanda ke neman horar da shugabannin ra’ayi a cikin Musulmai domin yaki da cin zarafin mata a arewacin Najeriya.
Sarkin ya yaba da shirin, yana mai cewa ya zo a kan gaba kuma ya dace da lokaci. Ya bukaci kungiyoyin da su taimaka wajen farfado da Dokar Iyali ta Jihar Kano wadda, a cewarsa, na dauke da muhimman matakan shari’a da za su kare mata da iyalai daga cin zarafi.
“Dukkan dokokin da ake bukata tuni suna cikin littattafan fikhu na Musulunci. Abin da ya rage shi ne a tara su a dunkule su a matsayin tsari daya da za a iya amfani da shi,” in ji shi.
Yayin da ya ke tunawa da binciken da ya gudanar a matsayin dalibi, Sarkin ya bayyana cewa kundin digirinsa na digiri na uku (PhD) ya mayar da hankali ne kan tsara dokokin iyali na Musulunci, inda ya yi nazari kan kotunan Shari’a tara a Kano na tsawon shekaru biyar. Sakamakon binciken ya nuna yadda ake yawan cin zarafin mata a fadin jihar.
A karshe, Sarkin ya ja kunnen shugabannin gargajiya, yana mai cewa: “Na umurci dukkan dagatai da hakimai cewa duk wanda aka samu da laifin dukan matarsa zai rasa sarautar gargajiyarsa.

