Bayan cece-kucen da ya biyo bayan kudirin sake fasalin haraji, shugaba Bola Tinubu ya umurci ma’aikatar shari’a da ta hada kai da majalisar dattawa domin yin gyare gyare sakamakon yadda Yan Arewa suka fusata .
Shugaba Tinubu wanda ke kasar Afirka ta Kudu, ya ba da umarnin sake duba kudirin ne yayin da wasu matasan arewacin kasar nan suka mamaye majalisar dattawa domin nuna goyon bayansu ga kudirin.
Kudurorin Dokar Harajin Najeriya ta 2024, da Dokar Kula da Harajin Najeriya, da Dokar Ma’aikatar Kudi ta Kasa da Dokar Karin Haraji sun haifar da zazzafar muhawara musamman a Arewa.
Masu sukar sun yi zargin cewa sauye-sauyen na iya kawo cikas ga daidaiton tsarin tarayya na kasafin kudi, da kuma yuwuwar karkatar da hukumar haraji da rage kudaden shiga na jihohi.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Muhammad Idris, mai take,n ‘Shugaba Tinubu ya jajirce wajen bin ka’idojin haraji,da jin koken jama’a.
A wani taro da aka yi a ranar 28 ga watan Oktoba, gwamnonin jihohin Arewa 19, a karkashin kungiyar gwamnonin Arewa, sun yi watsi da sabon tsarin rabon harajin da ake neman amincewa dashi.

